KALMOMIN JAKADA —MA DA WA — A RUBUTUN HAUSA: BITAR DOKOKIN HACFEWA DA RABAWA
Date
Authors
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Abstract
Jakada dai ajin kalraonii ne na nahawu guda biyu: wa/ma da suke Rulla dangantaka ta hanyar shiga tsakanin kalmar aikatau (so-kar6au) da kar6au tsayayye da kuma karBau ratayayye a cikin jimlolin Hausa. Yayin da - wa - take iya kar6ar bakuncin kalmomin madubi (irin su kaina, kanka, kanki, kansa, kanta, kanmu, kanku, kansu) tare da kowane irin suna a matsayin kar6au tsayayye da ratayayyen karbau a cikin jimla, ita kuma - ma - marabtar tsayayyen wakilin suna (irin su ni, kai, ke, shi/sa, ita, mu, ku, su) tare da kalmar suna a matsayin kar6au tsayayye da kar6au ratayayye take yi a tsari irin na gina jimloli a Hausa. Kusan dukkanin ayyukan da magabata suka yi, musamman ma na Institute of Education (1979), da Bunza (2002), da wasunsu sun fi karkata ga dokar -wa - ne kurum ba tare da sun yi tsokaci sosai game da - ma - ba. Ta yadda maimakon su (fora bisa dokoki da tsari iri daya da na ‘yar’uwarta sai suka rinka kai ta wani bigire na daban. Ta yin la’akari da aiki irin na nahawu, da tsari, da irin gurbin da kalmomin biyu - wa/ma - suke iya cikewa a cikin jimlolin Hausa, to za a gane dacewar tsayar da dokokinsu domin su zamanto iri daya. Saboda ba wani abu ne ya bambanta su ba face ita wannan tana tafiya ne jere da kalmar madubi tare da suna, yayin da ita kuma wancan take zuwa da wakilin suna tare da kowane irin suna a cikin jimloli. Bisa haka ne a wannan takarda aka yi waiwaye domin yi wa tsarin da ake kai a da garambawul dangane da wannan bayani na sama kan cewar kamar yadda ake ware jakada - wa - daga jikin kalmar aikatau idan -wa- din ta gabaci kalmar madubi, ko suna, tare da wani sunan to haka ma za a raba jakada -ma- (mi, mu, ma) daga jikin wakilin sunan da ake lifca ta. Sannan kuma ba za a hade ta da kalmar aikatau din da take gabanta ba, kamar yadda hukuncin - wa- yake a dokoki na nibutu irin na Hausa.