KARFAFAWA A SIGAR NASON SAUTI A HAUSA: NAZARI A WASU WAKOKIN MUSA DANKWAIRO
Date
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Abstract
Wannan takarda ta yi nufin zakulo wurare daban-daban da Rarfafa sauti yake zamtowa a sigar naso a cikin wasu wakokin makada Musa Dankwairo Maradum. An yi amfani da Diwanin Gusau (2019) wajen tattara wakokin da aka yi amfani da su, inda aka sami wurare masu yawa da Dankwairo yakan karfafa sauti ya rage masa daraja a ma’aunin amo a kokarinsa na nashe wasu sautuka da suka yi makwabtaka da juna. Domin tantance bayanai a kan nason an haka, an yi amfani da ma’aunin amo na Silkirk (1984) wajen auna yadda Rarfafawar take kasancewa. Saboda haka, nashe sauti tamkar rage masa daraja ne. Binciken ya gano cewa, nason dama na kalma da kalma yakan auku a cikin wakokin makada Musa Dankwairo, inda darajar kwayar sauti ta asali takan a ragu yayin da aka nashe ta.