<link rel="stylesheet" href="styles.f3b1fba60ec7970c.css">
Nasarawa State University, KeffiNasarawa State University, KeffiInstitutional Repository

Waiwaye a Kan Matakan Samar da Zaman Lafiya a Wasu Zubin Diyan WaJtoicin Makadan Baka na Hausa

Loading...
Thumbnail Image

Journal Title

Journal ISSN

Volume Title

Publisher

Department Of Nigerian Languages, Faculty Of Arts, Nasarawa State University, Keffi.

DOI

Abstract

Manufar wannan takarda ita ce fito da yadda wasu makadan baka na Hausa suke amfani da hikima wajen fadakar al’umma, musamman shugabanni wasu hanyoyin da za su iya amfani da su wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a Nijeriya. A wannan takardar an yi amfani da wani bangare na ra’in hanyar nazarin wakar baka ta Hausa da Gusau (2003-2014) ya tsara a littattafansa guda biyu ‘Jagoran Nazarin Wakar Baka’, da kuma ‘Wakar Baka Bahaushiya’, a ra’in an yi amfani da 6angaren da shafi nazarin falsafar alamomin rayuwar al’umma (Social-Semiotic Theory) An za6i yin amfani da wannan 6angare na ra’in ne, saboda yana da dangantaka da wannan takarda ta fuskar nazartar abubuwan da suka shaft rayuwar al’umma kai tsaye. Haka kuma, an yi amfani da wasu hanyoyi na bincike da suka hacfa da waiwayen ayyukan magabata musamman Diwanai na wakokin baka na Hausa inda aka tsattsamo misalan wuraren da makadan suka yi magana, a kan wasu matakai da hanyoyi da za a yi amfani da su wajen samar da zaman lafiya. Haka kuma, an tattauna da masana da manazarta domoin samun karin haske. Takardar ta gano diyan wakokin makadan baka na Hausa cike suke da hanyoyin samar da zaman lafiya ta fuskoki daban-daban. Haka kuma, takardar ta gano wasu muhimman batutuwan da makadan suka fi mai da hankali a kansu wajen samar da zaman lafiya a Nijeriya da suka hada da addu’a da hakuri da riko da noma da riko da gaskiya da kuma riko da ayyukan ibada da makamantansu.

Description

Citation

Buba, Abdullahi & Haruna, Iliyasu Makera (2022) Waiwaye a Kan Matakan Samar da Zaman Lafiya a Wasu Zubin Diyan WaJtoicin Makadan Baka na Hausa

Collections

Endorsement

Review

Supplemented By

Referenced By