<link rel="stylesheet" href="styles.f3b1fba60ec7970c.css">
Nasarawa State University, KeffiNasarawa State University, KeffiInstitutional Repository

Matsalar Daidaitacciyar Hausa:

Loading...
Thumbnail Image

Journal Title

Journal ISSN

Volume Title

Publisher

Department Of Nigerian Languages, Faculty Of Arts, Nasarawa State University, Keffi.

DOI

Abstract

Wannan makala ta yi bayani ne a kan irin cin dunduniya da kafafen watsa labarai na Rasashen Waje masu yin shirye-shirye da harshen Hausa suke yi wa Hausa. Wato, ba su lura da wasu Ra'idoji ko dokoki na harshen ba. Hakan ya sa aka rubuta wannan muRala a kan matsalar daidaitacciyar Hausa a kafafen watsa labarai na Rasashen waje. Daidaitacciyar Hausa dai ita ce Hausar hukuma, ita ce aka yarda a yi amfani da ita a hukumance. Kafafen watsa labarai hanya ce ta yin amfani da akwatin radiyo domin isar da saRo ta hanyar iska. Kafafen watsa labarai na Kasashen Waje masu yin shirye-shirye da Hausa, kafafen ne da mafi akasarinsu suke a yanki Turai. Tun lokacin da al'umma ta fara yawa, duniya tana ci gaba, kuma buRatu suka Rara Raruwa. A irin wannan lokacin ne, Turawa domin biyan buRatun kansu musamman a yankin Afirkan ta Yamma, a inda mafi yawa Hausawa ne don haka sai Turawa suka samar da wasu kafafen watsa labarai a yankunansu, suna watsa labarai da harshen Hausa, yana zuwa a ta hangar iska, domin Hausawa su ji kuma su riRa sanin halin da duniya take ciki. Labari bayani ne na wani abu da ya faru ake son a bayyana shi ga jama'a. Labari na kafafen watsa labarai ya bambanta da zantuka na yau da kullum. Domin sai ya hau wasu matakai kafin ya zama labari, kamar tushe ko ginshiRi (kafar sadarwa), da kuma saRo, sai kumu hanyar ta sadarwa (iska), da samun masu sauraro, sannan kuma a sami sakamako, irin wannan shi ne hanyar samar da labari a kafafen watsa labarai.

Description

Citation

Mohammed, Yusuf & Buba, Abdullahi (2021) Matsalar Daidaitacciyar Hausa: Tsokaci a Kan Kafafen Watsa Labarai Na Kas ashen Waje

Collections

Endorsement

Review

Supplemented By

Referenced By