Tasirin Harshen Hausa A Rubuce-Rubuce A Jikin Abubuwan Hawa Na Sufuri A Ma'aunin Sana'a Da Fadakarwa
Loading...
Files
Date
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Department Of Nigerian Languages, Faculty Of Arts, Nasarawa State University, Keffi.
DOI
Abstract
Masana da manazarta sun bayyana harshe da cewa, wata banyar sadarwa ce, ta yadda dan’adam yake amfani da sautuka ko wasu alamomi masu ma ’ana, wanda kuma yake bin wasu dokoki da ka ’idoji na musamman domin cim ma burin isar da sako. Batun da aka yi magana a wannan takarda shi ne. Tasirin Harshen Hausa a Rubuce- Rubuce a Jikin Abubuwan Hawa na Sufuri a Ma’aunin Sana’a da Fadhkarwa. Manufar wannan takarda ita ce fito da gudummawar da harshen Hausa yake bayar a rubuce-rubucen da ake yi a jikin abubuwan hawa na sufuri ta fuskar sana ’a da fadakarwa. Haka kuma takardar ta (fora rubuce-rubucen a kan mizani ko magwaji na sana ’a da fadakarwa domin a fito da tasirin da harshen Hausa ya bayar musamman ta fuskar samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai. Bayan liaka, takardar ta fito da muhimmancin rubuce-rubucen ta bangaren sana ’a da fadakar da afumma. A wannan takarda an yi amfani hanyoyi da dabam na bineike da suka haefa da ziyartar tashoshin matoci da tattaunawa da masu yin rubuce-rubucen da kuma tattaunawa da masu abubuwan hawa. Samian kuma, an duba waefansu Iittattafai da suke da alaka da takardar. Haka kuma an yi amfani da salon sharhi a karkashin kowane misali da aka kawo. Sakamakon wannan bineike ya gano cewa, rubuce-rubucen da ake yi da harshen Hausa a jikin abubuwan hawa na sufuri suna taimaka wa matasa wajen samun abin dogaro da kai (sana’a). Haka kuma yawancin rubuce-rubucen da aka tattaro suna dauke ne da sakon fadakarwa ga fasinjoji da kuma sauran afumma ta fuskar tarbiyya dangane da ladabi da biyayya da hakuri da gaskiya da kuma riko da addu ’a.
Description
Citation
Buba, Abdullahi & Haruna, Iliyasu Makera (2021) Tasirin Harshen Hausa A Rubuce-Rubuce A Jikin Abubuwan Hawa Na Sufuri A Ma'aunin Sana'a Da Fadakarwa
