<link rel="stylesheet" href="styles.f3b1fba60ec7970c.css">
Nasarawa State University, KeffiNasarawa State University, KeffiInstitutional Repository

Nazarin Tubalan Ginin Turke a Wakar ‘Matar Jami’a' ta Nazir Muhammad Ahmad Sarkin Waka

dc.contributor.authorBuba, Abdullahi
dc.contributor.authorMuhammad, Mukhtar Sadauki
dc.date.accessioned2023-11-02T13:46:29Z
dc.date.available2023-11-02T13:46:29Z
dc.date.issued2022-11-14
dc.description.abstractA wannan takarda batun da aka yi magana a kansa shi ne ‘Nazarin Tubalan Ginin Tuke a Wakar Matar Jami’a ta Nazir Muhammad Ahmad. Manufar wannan takarda ita ce, fito da yanayin tubalan da Nazir ya yi amfani da su a wakarsa ta matar jami’a wajen isar da sakonsa ko manufar wakar ga al’umma. Don cim ma manufar da aka kudurta, takardar ta yi nitso a cikin wakar ta hanyar zakulo wasu batutuwa da ake ganin su ne muhimman tubalan ginin turken wakar day a shafi fadakar da al’umma, a kan yanayi da matsalolin karatun wasu mata a jami’a. A wannan takarda an yi amfani da ra’in nazarin wakar baka Bahaushiya, da Gusau (2003 & 2014) ya gabatar a littattafansa guda biyu. Jagoran Nazarin WaRar Baka da Wakar Baka Bahaushiya. Takardar ta yi amfani da wasu hanyoyi da dabarun gudanar da bincike da suka hada da amfani da matanin wakar da kuma duba wasu littattafai da makalu da suke da alaka da takardar. Takardar ta gano babban turken wakar facfakarwa ce, ga iyaye a kan yanayi da matsalolin karatun mata a jami’a. Sannan kuma, takardar ta gano wasu muhimman batutuwa a matsayin tubalan ginin turken wakar da suka hada da buri da kwadayi da tarbiyya da amana da hakuri da kuma tsoron Allah. Bayan haka, takardar ta gano tubalan ginin turken wakar, sun fito da yanayin rayuwar wasu mata a jami’a, musamman ta yadda suke daukar dala ba gammo, ta hanyar koyi da rayuwar wasu kawayensu.en_US
dc.identifier.citationBuba, Abdullahi & Muhammad, Mukhtar Sadauki (2022) Nazarin Tubalan Ginin Turke a Wakar ‘Matar Jami’a' ta Nazir Muhammad Ahmad Sarkin Wakaen_US
dc.identifier.urihttp://localhost:8080/xmlui/handle/123456789/9231
dc.language.isoenen_US
dc.publisherDepartment Of Nigerian Languages, Faculty Of Arts, Nasarawa State University, Keffi.en_US
dc.subjectTubalin Ginin Turke; Matar Jami’aen_US
dc.titleNazarin Tubalan Ginin Turke a Wakar ‘Matar Jami’a' ta Nazir Muhammad Ahmad Sarkin Wakaen_US
dc.typeArticleen_US

Files

Original bundle

Now showing 1 - 1 of 1
Loading...
Thumbnail Image
Name:
14. December (2022).pdf
Size:
1,023.38 KB
Format:
Adobe Portable Document Format
Description:

License bundle

Now showing 1 - 1 of 1
Loading...
Thumbnail Image
Name:
license.txt
Size:
1.71 KB
Format:
Item-specific license agreed upon to submission
Description:

Collections