Tsokaci A kan Gyaran Hali A Wasu Diyan Wakokin Musa Dankwairo
Loading...
Files
Date
Authors
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Department Of Nigerian Languages, Faculty Of Arts, Nasarawa State University, Keffi.
DOI
Abstract
Wannan takarda ta yi nufin nazarin siffofin gyaran hali a wasu Wakokin Alhaji Musa Dankwairo Maradun. Manufar wannan takarda ita ce nazarin yadda makada Dankwairo yake amfani da hikima wajen cfora al’ummar da yake zaune cikinta a kan turba ta kwarai ta hanyar jawo hankalin al’ummar a kan aikata kyakkyawa da kuma kauce wa munana. Domin samun hasken gudanar da wannan takarda an yi amfani da hanyar nazarin wakar baka ta Hausa da Gusau (2003 da 2014) ya tsara. Hart yau domin kwalliya ta biya kudln sabulunta, an yi nazarin da saurao na kwakkwafi na wasu wakokin Dankwairo wadanda aka samu a cd . Bayan nan an juiti wasu wakokin cikin tsarin rubutun Hausar book. Wasu wakokin kuma an same su ne daga Gusau (2019) Diwanin Wakokin Baka Juzu’i na Hucfu.. Binciken ya gano, wasu wakokin Dankwairo cike suke da nason facfakarwa ta fuskar umumi da kyakkyawa da hani da munana. Haka kuma, takardar ta fito da muhimman abubuwan da Dankwairo ya fi mai da hankali a kansu musamman wadanda suka shaft rayuwar al’ummata yau da kullum. Haka nan, binciken ya lura akwai wurare guda bakwai (7) da suka shaft umumi da kyakkyawa da kuma wurare guda uku (3) da suka shaft hani da munana.
Description
Citation
Buba, Abdullahi & Mohammed Yusuf (2023) Tsokaci A kan Gyaran Hali A Wasu Diyan Wakokin Musa Dankwairo
